Thursday, January 19, 2017




Zan Canja Jiha Muddin Ba Za’a Kula Da Mu -------Dan Gudun Hijira

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Wani xan gudun Hijirar Talala dake yanki Buni Yadi, Alhaji Ari Talala ya bayyana cewa shi kan a shirye yake da ya canja jiha ya zama dan Gombe tunda shugabanin da suka zaba basa tausayawa irin halin da suke ciki na quncin rayuwa.

Alhaji Ari Talala, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Gombe inda yace sun sa kuri’a sun zave Sanatansu Ali Ndume da yar Majalisar tarayya Asabe Bileta kuma sun zavi shugaban qasa Muhammadu Buhari, amma anqi kulawa dasu an barsu a suna ta gudun hijira.

Yace shi kan zai iya canja jiha yabar Dajin da suke xin nan saboda babu hanya kuma har yanzu akwai Maharan nan na Boko Haram a wajen saboda haka a xauki matakin farko na samar da hanya da zai kawo qarshen wadannan mutane.

Dan gudun hijirar ya qara da cewa zamansu a wannan Jeji na Talala ba zai kai    su ba saboda idan ba’a san yadda za’ayi a kawar da waxannan Yaran ba babu yadda za’ayi su koma wannnan gari  su zauna.

Ari Kaku, ya kuma ce garuruwan da suke wannan yanki na Talala da Ajigin da Gwargore da Kaba nan ne Yan Boko Haram din suka dawo bayan tarwatsasu da akayi daga Dajin Sambisa.

A cewarsa abunda yasa yake cewa zai canja jiha shi ne saboda shugabanin da suka zaba babu wanda ya taba zuwa ya nemesu a Gombe da suke gudun hijira don ya taimakesu amma da buqatarsu ta taso na neman kuri’u ai har inda suke xin a Gombe aka turo motoci aka xaukeso suka je sukayi zave amma yanzu an manta dasu.

“Muna fama da matsalar tsadar rayuwa da kuxin gidan haya ga babu sana’a muna fama da quncin rayuwa kuma anqi a kula damu ai dole ma ranmu zai vaci saboda ba’a xauke mu muna da amfani ba, “inji Ari Kaku.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnonin jihohin Borno da Yobe da cewa su haxa kai suyi dukkan mai yiwuwa wajen ganin sun mayar da duk wani xan gudun hijira inda ya fito tunda yanzu an fara samun zaman lafiyar da ake ganin zai dore.



Xxx