Thursday, August 4, 2011

KIRA GA MA SHAYA TABA SIGARI

BUDADDIYAR WASIKA

KIRA GA MA SHAYA TABA SIGARI

Biyo bayan sanarwar da kamafonin da suke Sarrafa Taba Sigari, su ka yi wa jama’a na fada masu cewar ita wannan Tabar Ma’aikatar kiwon Lafiya ta kasa ta yi gargadin cewar shanta hatsari ne ga rayuwa kuma mashayanta suna iya mutuwa tun da kuruciyarsu, sannan aka lika a jikin kwalin Tabar amma duk da haka muka ki ji wajen yin kunnen uwar shegu na saya da kudin mu, mu sha.

Da wannan sanarwa da kamfanonin da suke sarrafa Tabar suka yi na ke son in dauki wannan damar wajen yin kira ga dukkan daukacin jama’a da sukan sha Taba Sigari, a bayynar jama’a da cewar su dai na domin bai dace ba saboda wanda baya shan Tabar idan ka busa ma shi hayakin Tabar za ta cutar da shi kuma ka dauki alhakinsa wajen cutar da lafiyar sa.

Sannan kuma ina son in kirayi gwamnati da babbar murya wajen daukar nauyin fadakar da masha ya Taba Sigari, ko a Jaridu ko a gidajen Radiyo, ko a Talabijin ne cewar dukkan mai shan Taba ya kaurace gefe guda domin shan ta a cikin jama’a akwai cutarwa, ga wadanda ba sa sha amma duk wanda ya yi kunnen uwar shegu da wannan sanarwa sai gwamnati ta hukunta shi.

Har yanzu kuma kamar wadanda suke tafiya suna shan Tabar a kan hanya hakan bai dace ba domin a tafiyar da kake yi din za ka iya wuce wani a daidai lokacin da ka busa hayakin nan ka ga ka busa ma shi, kuma ai kamar yadda mutum ba zai dinga tafiya yana cin abinci ba to ta ya ya zai dinga tafiya ya na shan Taba, ai hakan ma zai kara zubar masa da mutunci a idon jama’a.

Ina kuma so in sake kira ga gwamnatin tarayya na cewar ta yi dukkan mai yi wuwa wajen ganin ta magance wannan matsala ta Shan Taba a cikin jama’a duk da cewar mai shan Taba da zarar ka fa da masa cewar shan Taba babu kyau zai fara ce maka ai Likitoci ma suna Sha, abin tambaya a nan shine don Likita yana shan Taba shi kenan sai kai ma ka sha Taba,? ko kuma ka ji mutum yace maka ai ba haram bace almumbazzaranci ne, almumbazzaranci abin yi ne, ga musulmi ai Addinin Musuluci ya fada mana cewar dukkan almubazzari abokin Shaidan ne to wa yake so ya zama abokin Shaidan.

Ma’aikatan Lafiya, sun tabbatar da cewa wanda ba ya shan Taba Sigari, idan mai shan ta, ya busa ma shi hayakin shi wanda ba ya sha din yafi cutuwa da illar ita Taba din.

Abin tambaya ma a nan shine menene ya sa jama’a ba za su kiyaye lafiyar su ba, tunda su kansu kamfanonin da suka yi yo Tabar nan sun fada cewar ta na da hatsarin gaske ga rayuwa amma muke shan ta, ba fa abinci bace ko kuma ibada bace ba balle muce ta zama mana dole sai mun sha?.

Ni dai fata na a nan shine na riga nasan babu yadda za’a yi adai na shan Taba Sigari, amma abin roko shine adaina shanta a cikin jama’a ko kuma shanta barkatai a wuraren da ba su dace ba, sai dai muna fatan tunda shan Taba hatsari ce ga rayuwa, Allah ya kawo karshen shan ta ga jama’a tunda ba magani ba ce don ka sha kace za ta maka maganin ciwon kai ko ciwon ciki ko ma kace za ta hana ka jin yunwa, in kuma ba haka ba to ina fata Allah ya sa masu shan ta su san cewa ba ta da wani amfani ga rayuwarsu sai ma lalatar masu jiki su yi bagi ga bakin baki sannan kuma ga rage masu daraja da kima a idon jama’a.

End.


Daga ABUBAKAR RABILU, Bolari Gombe
G.S.M 080-36597674, 080-28094624
I mail: - rabiluabubakar@yahoo.

NASIHA GA `YAN KASUWAR KASAR NAN KAN TSAUWALA FARASHIN KAYAYYAKNN MASARUFI A WATAN AZUMI.

BUDADDIAR WASIKA
 
NASIHA GA `YAN KASUWAR KASAR NAN KAN TSAUWALA FARASHIN KAYAYYAKNN MASARUFI A WATAN AZUMI.

Assalamumualaikum ya `yan Uwana  Musulmi `yan kasuwa a wannan kasatamu mai albarka Najeriya qasar da ita muka sani muke tunqaho da ita ina so inyi mana nasiha `yar kaxan game da yadda ake yawan qare-qaren farashin kayayyaki masarufi  a wata mai cike da alfarma da ximbin lada watan Ramadan.

 ina so in xan ja kunne `yan kasuwan mu kan irin yadda suke yawaita qare-qaren farashin kayayyakin masarafu da zarar watan Azumi na Ramadan ya tsaya wajen tsauwala farashin duk wani abu da mai azumi zai bukata sai kaga kudin sa ya qaru anya kuwa ladan muke nema wajen Allah.

Ya Jama'a ina so ku gane cewar idan watan Azumi ya tsaya kamata ya yi a rage farashin kayayyaki koda mun saye da tsada saboda alfarmar watan tunda wannan qasa tamu mu musulumi muke da kashi saba'in cikin xari na yawan jama'a amma sai gashi babu lokacin da farashin kayayyakin masarafu ke hauhawa sai a watan azumi watan neman lada babu kuma lokacin da farashin kayak e sauqa sa a watan Disamba na Kirsimeti hakan shine kishi ga musulmi.
Idan haka ne muna koyi da sahabai kuwa wadanda suke sadaukar da dukiyoyin su gaba daya ga jama'a mabuqata da zarar watan azumi ya tsaya domin neman falalar Ubangiji a ranar gobe alqiama, mu kuwa `yan kasuwa babu abun da muke yi sai qara farashin kayayyaki domin ganin an tozartar da mai yin azumi musammam ma a irin wannan yanayi da rayuwa tayi tsada.

Anya kuwa muna son idan muka mutu mu hadu da rahamar Ubangiji da muke ta fada a baki da bai kai har zuci ba, jama'a mu farka mu gyara halayen mu muddin muna neman jin qai a wajen Ubangiji ranar gobe.

Ya ku `yan kasuwar kasar nan wallahi kalubalenku ga tambaya ta a gareku na neman sanin wace hujja kuka dogara da ita na kara farashin kayayyaki da zarar an fuskanci watan azumin ramadan?. Ku bani amsa daga ina farashin yake qaruwa daga kamfanoni ne ko daga wajen ku.

Wallahi `yan kasuwa idan kuna begen kaucewa azabar Allah ranar gobe ku cire son zuciya da neman abun duniya ta kowacce irin hanya na tsauwala farashin kayayyaki da kuke yi a watan da aka bude kofofin gidan aljanna aka ce ba mai shiga sai azumi ku kuma kuke fada da mai yin azumin.

Ya ku `yan kasuwa idan kuna da kishi da kuma qaunar ganin kun samu falalar wannan watan me yasa kuke qara farashin Sukari da kashi hamsin, Lemon zaki na sha kowanne daya shima sai kun qara masa kudi menene hujjar ku tayin hakan?. `yan kasuwa baku da hujja idan akwai ta ina sauraro.

Wani abun ban takaici a wannan kasa tamu da muke ikirarin kishin ta a baki mu da muke azumi munfi wadanda basa azumi yawa amma masu azumi sune ke qara farashin komai a lokacin azumi, domin neman duniya su kuma wadanda basa azumi da zarar nasu watan hidimar ya kama wato na Kirsimeti ko na sabuwar shekara farashin komai rage shi suke yi da kamar kashi hamsin domin kowa yaga ya samu abun da zai rufawa kansa asiri.

Ya `yan uwana dukkan wanda ya karanta wannan mukala tawa ya isheni zama shaida akan `yan kasuwa na abun da na fadi a ciki domin kuwa idan watan hidimar wadancan mabiya ya tsaya duk inda ka shiga a fadin jihar ku, za kaga daga shagunan sayar da kaya zuwa bankuna har da Ma'aikatu na gwamnati ana maka barka da zuwa da wannan wata ko shekarar ta hanyar sanya wadansu kyallaye ko wuta masu qyalqyali kuma farashin komai za kaga sun rage, me yasa mu da muke da rinjaye ba zamu yi hakan ba don ayi koyi da mu, tunda mu ba zamu yi koyi da su ba.

Har ila yau ina son in shaidawa mai karatu cewa duk wani abun ban haushi da takaici da yake faruwa a doron kasar nan mutanen mu su suke aikata shi amma idan abu na kirki da nuna sanin ya kamata ne har ga Allah an barmu a baya wannan ba abun bakin ciki bane?

Ba zan gajiya ba ina nan ina mai kira ga `yan kasuwa kan irin yawan bala'in da yake fada masu inma na gobara ko na `yan fashi wallahi ba wani abu ke haifar da hakan ba illa rashin tsabtar kasuwancin su, domin irin wannan bala'i da masifar su suke janyowa kansu ta hanyar qare-qaren farashin kayayyaki a lokutan samun lada wanda kuma fa ba’a qara musu kudin a can inda suke sayowa ba, inda duk a watanin da muke dasu goma sha biyu babu mai cike da lada da albarka kamar watan Azumi na Ramadan amma su kuwa shine suka tara su zaba domin tozartar da mai azumi ta hanyar tsauwala masu a dukkan nau'ukan kayayyakin abincin da za su ci.

Ba ina yiwa `yan kasuwa mugun fata bane, gaskiya ce wacce aka ce daci ne da ita shi yasa a cikin al'umma idan kaga bala'i ya aukawa `yan kasuwa talakawa basa jajanta masu saboda irin halin da suka jefa talakawa a ciki.

Ya ku `yan kasuwa saboda bala'in da kuke jefa talakawa a ciki na tsadar kayayyaki hatta kai a masallatai ana ta addu'ar neman Allah ya kawo sauki domin wannan masifa ce ba ‘yar karama ba a tsakanin al'umma.

Jama'a ku duba halin da talakawa suke ciki bayan ga tsadar rayuwa sannan ga shi dan abun da mai azumi zai nema a lokacin azumi yaci mai kyau don qarin kuzari a jikin sa da kuma kara masa lafiya yafi qarfin sa a wannan kasa tamu da muke ikirarin cewar ita ce Uwa a qasashen Afirka.

Idan zamu fadawa kanmu gaskiya ba kowanne lokaci ne Shugabani suke da laifi a kan talakawa ba wata masifar mu ne da kanmu muke janyo ta idan tafi qarfin mu ne sai mu dora ta akan shugabanni, bayan kuma kowa na son ya samu sauki amma `yan kasuwa basa so domin su kanje su sayo kaya da sauki su kuma sai su ki sayarwa da sauki sai da tsada kaga haka ai ba adalci bane ko kadan.

Da dan wannan kira nake son ince wa Mai karatu ba zan so in yi dogon bayani ba domin kafin in fada wasu da yawa sun fada don haka kirana anan ga `yan kasuwa shine aji tsoron Allah wajen harkar kasuwanci a sanya gaskiya kuma kar son dukiya ya jefa mu ga halaka a ranar qin dillanci wato ranar gobe da kowa zai bada bahasin abun da ya aikata da kansa.

Rabilu Abubakar, Masharhanci ne kan al'amuran yau da kullum  ya rubuto ne daga Unguwar Bolari a fadar jihar Gombe.

GSM: - 080-36597674
             080-28094624
Imail: -
rabiluabubakar@ yahoo.com
 
 

Monday, June 6, 2011

Kukan kurciya

Assalamu alaikum jama'a
Zan turo da wani darasi mai suna kukan kurciya nan gaba kadan da zarar na kammala