Yau za'a fara sauraron ra'ayoyin jama'a kan batun karin albashi na shiyar arewa maso gabas a Gombe.
By Rabilu Abubakar, Gombe
A yau Alhamis ne Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kafa dan sauraron ra'ayoyin jama'a game da karin mafi karancin albashi zai fara sauraron ra'ayoyi jama'a na shiyar arewa maso gabas a Gombe.
kwamitin karkashin jagorancin mataimakin shugaban kungiyar gwadago ta kasa NLC Mista James Peter Adeyemi da taimakon shugaban kungiyar gwadagon na jihar Gombe.
taron jin ra'ayoyin jama'ar zai gudana ne a babban otel din nan na kasa da kasa dake Gombe inda ake sa ran gwamnonin jihohin arewa maso gabas da kungiyoyin lauyoyi da na ma'aikata da sauran su za su halarta har ma da daidaikun jama'ar gari.
ku biyo mu dan jin yadda taron zai kasance.
No comments:
Post a Comment