Sunday, February 2, 2014

INA SHARE KWANAKI UKU BA CI BA SHA A ZAMANA NA GIDAN YARI----MANJO AL-MUSTAPHA



INA SHARE KWANAKI UKU BA CI BA SHA A ZAMANA NA GIDAN YARI----MANJO AL-MUSTAPHA

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe

Tsohon dogarin tsohon shugaban qasar Najeriya Manjo Hamza Al-Mustapha wanda ya shafe shekaru goma sha biyar yana zaman gidan kurkuku a qasar nan ya bayyana irin yadda zamansa a gidan kurkukun ya kasance cikin azabar da   ya sha game da zama da ishiruwa da yunwa.

Manjo Al-Mustapha, ya bayyana cewa yana zama na wasu kwanaki da basu gaza uku ko huxu ba ba tare da an bashi abinci ko ruwan sha ba har ya gama zamansa na gidan kurkuku ya fito.

Manjo Hamza Al- Mustapha, wanda shine jagoran wata qungiya mai suna AFUDY ya bayyana hakan ne a lokacin da ya zo jihar Gombe don jaddada muhimmancin wannan qungiya ta sa mai suna AFUDY wacce yace ya kafata ne don samarwa da matasa aikin yi a faxin qasar nan.

Manjo Al-Mustapha, yace tun bayan fitowarsa daga gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni na shekara ta 2013 yake yawo don zaga jihohin qasar nan wajen ganin ya gana da masu ruwa da tsaki don shaida musu aniyar sa ta ceto qasar nan daga halin da take ciki musammam ma yankinsa da ya fito na arewa maso gabas wanda yake qoqarin ganin ya ceto matasan yankin.

Ya kuma ce kafin a tsare shi a gidan yarin shekaru goma sha biyar da suka gabata yana yawo ba dare ba rana yana zaga qasar nan saboda yana aiki da qungiyoyi masu yawa kama daga kudancin Najeriya har zuwa arewaci don ganin an ceto matasa.

A cewar sa a shekara ta 1984 ne yasa kansa a cikin wata qungiya inda suke faxi tashin ganin sun taimakawa waxanda suke da buqatar hakan wanda burinsu shine na ganin an samu al’umma wacce take da tarbiyaa da xa’a wacce ba za’a sameta da rikici na tashe-tashen hankula ba wanda a lokacin da aka kamashi aka tsare shine wasu qungiyoyin sun tsaya amma yanzu da ya fito shine yake ci gaba.

 Manjo Hamza Al-Mustapha, ya kuma xan bada bayani halin quncin rayuwar da ya shiga a gidan Yarin na rashin samun abinci da ruwan sha wanda sai ya yi kwanaki sannan a ba shi sau xaya. Amma a cewar sa akwai wani Soja xan asalin jihar wanda yake taimaka masa da ruwa da abinci a boye amma Allah ya yi masa rasuwa a wani lokaci da yaje nemo masa qosai da ruwa.

A boye wannan sojan yake tsallakewa ya fita da Babur xinsa ya nemo min ruwan leda na Pure water da abinci wata rana da qosai ya kawo min inci ba tare da an ganshi ba” inji Al-Mustapha.

Cikin jimami da qarfin zuciya Al-Mustapha, yace ranar da wannan Soja zai rasu yazo ya gaishe shi yace Oga bari inje in nemo maka abinci bayan munyi sallama dashi ya fita yaje ya nemo min qosai da ruwa akan babur xinsa yana dawowa sai ya yi hatsari yaji ciwo kafin ayi masa allura tetanus ya shiga wanda shine ya yi sanadiyar ajalinsa

 Daga nan ne sai yace bayan hidimar wannan qungiya tasa taimakon iyalan wannan Soja suna daga cikin dalilansa na zuwa Gombe don ya taimakawa iyalan wannan Soja bisa yadda ya dinga masa hidima da har kan ya zamo sanadiyar rayuwar sa.

            

Xxx

Alhaji Salisu Muhammad Gombe shugaban kungiyar Izala ta Gombe kuma Sakataren tsare-tsare na kungiyar yan Agajin Izala ta kasa tare da Babban Sakataren kungiyar yan agajin ta kasa Alhaji Abba Katsina a wajen taron Majalisar yan agajin na kasa a jihar Gombe a ranar Asabar 1 ga watan Janairu 2014 wanda ya dauki hoto Abubakar Rabilu.

KUNGIYAR IZALA TA GUDANAR DA TARON MAJALISAR ‘YAN AGAJIN TA NA QASA A GOMBE



QUNGIYAR IZALA TA GUDANAR DA TARON MAJALISAR ‘YAN AGAJIN TA NA QASA A GOMBE

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe

A makon nan ne qungiyar ‘yan agajin jama’atu Izalatul Bidi’ah wa’iqamatussunah ta gudanar da taron majalisar ‘yan agajin ta na qasa a jihar Gombe don tattauna matsalolin da suka shafi qungiyar.

Da yake yiwa manema labarain qarin haske kan maqasudin wannan taro babban Daraktan ‘yan agajin na qasa Injiniya Mustapha Imam Sitti, cewa ya yi qungiyar  ‘yan agajin Izala takan gudanar da irin wannan taro ne don shawo kan matsalolin da suka shafi qungiya da kuma irin ayyukan da zasu fuskanta a gaba.

Injiniya Mustapha Sitti, yace a lokacin irin wannan taro sukan faxakar da ‘yan agajinsu yadda zasu kula da maras lafiya a asibiti idan sun kai xauki  da kuma yadda za su bai wa wanda ya gamu da hatsarin mota agajin gaggawa da kuma bada tallafi a lokacin da aka samu hatsarin gobara.

A cewar sa a shekarar da ta gabata sun gudanar da irin waxannan ayyuka shi yasa yanzu suka sake taruwa don suga irin nasarorin da suka samu sannan su ga irin tsare-tsaren da za suyi a wannan shekara ta 2014.

Daraktan ‘yan agajin ya qara da cewa qungiyarsu ta ‘yan agaji sukan gudanar da irin wannan taro ne sau uku ko sau huxu a kowacce shekara sannan kuma su kan  gudanar da tarurruka na qarawa juna sani don qara karantar da mambobin  qungiyar  tasu ta ‘yan agaji don su sami makamar aiki da suke gudanarwa  a cikin wannan qasa.
  
Mustapha Sitti, ya kuma ce wannana qungiya ta ‘yan agaji ta samu nasarori da dama wanda babban nasarar da suka samu ita ce mutane suna fahimtar aikin da suke yi domin ko a lokacin aikin hajji hankalin jama’a bai kwanciya har sai sunga ‘yan agajin sannan suke bari a fara tantancesu a filin jirgin sama.

Ya kuma ce bama anan qasa Najeriya wannan qungiya tasu take aiki ba hatta a qasashe irinsu Saudi Arebiya da Benin da Ghana da Kamaru wannan qungiya ta kafu kuma tana taimakawa kuma a shekarar da ta gabata ma sunje har Saudi arebiya sunyi miti na qungiyar  wanda har gwamnatin qasar ta fahimci irin wa’azuzzukan da qungiyar take gabatarwa.

Injiniya Mustapha Sitti, ya nuna takaicinsa na rashin samun tallafi da qungiyar ‘yan agajin bata samu a lokacin da ya kamata musammam ma na kujerun aikin hajji da za su bai wa ‘yan agajinsu don taimakon Alhazai a can qasar Saudiya, inda yace da kamar yadda kowacce qasa da gwamnati take taimakawa Red Cross  haka ake taimakawa ‘yan agajin da basu da matsala.

Daga nan sai yace babban burin qungiyar a wannan shekarar shine suga ayyukansu sun qara faxaxa ta kowacce hanya don taimakon al’ummar musulmi.

Shi kuwa da yake tsokaci shugaban qungiyar izala ta jihar Gombe wanda kuma shine babban sakataren tsare-tsare na qungiyar ‘yan agaji ta qasa Alhaji Salisu Muhammad Gombe, godewa shugabannin qungiyar ya yi na yadda suka zavi jihar Gombe don gudanar da wannan taro.

Xxx