QUNGIYAR IZALA TA GUDANAR DA TARON MAJALISAR ‘YAN
AGAJIN TA NA QASA A GOMBE
Daga
Rabilu Abubakar, a Gombe
A makon nan ne qungiyar ‘yan agajin
jama’atu Izalatul Bidi’ah wa’iqamatussunah ta gudanar da taron majalisar ‘yan
agajin ta na qasa a jihar Gombe don tattauna matsalolin da suka shafi qungiyar.
Da yake yiwa manema labarain qarin haske
kan maqasudin wannan taro babban Daraktan ‘yan agajin na qasa Injiniya Mustapha
Imam Sitti, cewa ya yi qungiyar ‘yan
agajin Izala takan gudanar da irin wannan taro ne don shawo kan matsalolin da
suka shafi qungiya da kuma irin ayyukan da zasu fuskanta a gaba.
Injiniya Mustapha Sitti, yace a lokacin
irin wannan taro sukan faxakar da ‘yan agajinsu yadda zasu kula da maras lafiya
a asibiti idan sun kai xauki da kuma
yadda za su bai wa wanda ya gamu da hatsarin mota agajin gaggawa da kuma bada
tallafi a lokacin da aka samu hatsarin gobara.
A cewar sa a shekarar da ta gabata sun
gudanar da irin waxannan ayyuka shi yasa yanzu suka sake taruwa don suga irin
nasarorin da suka samu sannan su ga irin tsare-tsaren da za suyi a wannan
shekara ta 2014.
Daraktan ‘yan agajin ya qara da cewa
qungiyarsu ta ‘yan agaji sukan gudanar da irin wannan taro ne sau uku ko sau
huxu a kowacce shekara sannan kuma su kan
gudanar da tarurruka na qarawa juna sani don qara karantar da mambobin qungiyar tasu ta ‘yan agaji don su sami makamar aiki da
suke gudanarwa a cikin wannan qasa.
Mustapha Sitti, ya kuma ce wannana qungiya ta
‘yan agaji ta samu nasarori da dama wanda babban nasarar da suka samu ita ce
mutane suna fahimtar aikin da suke yi domin ko a lokacin aikin hajji hankalin jama’a
bai kwanciya har sai sunga ‘yan agajin sannan suke bari a fara tantancesu a
filin jirgin sama.
Ya kuma ce bama anan qasa Najeriya
wannan qungiya tasu take aiki ba hatta a qasashe irinsu Saudi Arebiya da Benin
da Ghana da Kamaru wannan qungiya ta kafu kuma tana taimakawa kuma a shekarar
da ta gabata ma sunje har Saudi arebiya sunyi miti na qungiyar wanda har gwamnatin qasar ta fahimci irin
wa’azuzzukan da qungiyar take gabatarwa.
Injiniya Mustapha Sitti, ya nuna
takaicinsa na rashin samun tallafi da qungiyar ‘yan agajin bata samu a lokacin
da ya kamata musammam ma na kujerun aikin hajji da za su bai wa ‘yan agajinsu
don taimakon Alhazai a can qasar Saudiya, inda yace da kamar yadda kowacce qasa
da gwamnati take taimakawa Red Cross haka ake taimakawa ‘yan agajin da basu da matsala.
Daga nan sai yace babban burin qungiyar
a wannan shekarar shine suga ayyukansu sun qara faxaxa ta kowacce hanya don
taimakon al’ummar musulmi.
Shi kuwa da yake tsokaci shugaban
qungiyar izala ta jihar Gombe wanda kuma shine babban sakataren tsare-tsare na
qungiyar ‘yan agaji ta qasa Alhaji Salisu Muhammad Gombe, godewa shugabannin
qungiyar ya yi na yadda suka zavi jihar Gombe don gudanar da wannan taro.
Xxx
No comments:
Post a Comment