Sunday, February 2, 2014

INA SHARE KWANAKI UKU BA CI BA SHA A ZAMANA NA GIDAN YARI----MANJO AL-MUSTAPHA



INA SHARE KWANAKI UKU BA CI BA SHA A ZAMANA NA GIDAN YARI----MANJO AL-MUSTAPHA

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe

Tsohon dogarin tsohon shugaban qasar Najeriya Manjo Hamza Al-Mustapha wanda ya shafe shekaru goma sha biyar yana zaman gidan kurkuku a qasar nan ya bayyana irin yadda zamansa a gidan kurkukun ya kasance cikin azabar da   ya sha game da zama da ishiruwa da yunwa.

Manjo Al-Mustapha, ya bayyana cewa yana zama na wasu kwanaki da basu gaza uku ko huxu ba ba tare da an bashi abinci ko ruwan sha ba har ya gama zamansa na gidan kurkuku ya fito.

Manjo Hamza Al- Mustapha, wanda shine jagoran wata qungiya mai suna AFUDY ya bayyana hakan ne a lokacin da ya zo jihar Gombe don jaddada muhimmancin wannan qungiya ta sa mai suna AFUDY wacce yace ya kafata ne don samarwa da matasa aikin yi a faxin qasar nan.

Manjo Al-Mustapha, yace tun bayan fitowarsa daga gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni na shekara ta 2013 yake yawo don zaga jihohin qasar nan wajen ganin ya gana da masu ruwa da tsaki don shaida musu aniyar sa ta ceto qasar nan daga halin da take ciki musammam ma yankinsa da ya fito na arewa maso gabas wanda yake qoqarin ganin ya ceto matasan yankin.

Ya kuma ce kafin a tsare shi a gidan yarin shekaru goma sha biyar da suka gabata yana yawo ba dare ba rana yana zaga qasar nan saboda yana aiki da qungiyoyi masu yawa kama daga kudancin Najeriya har zuwa arewaci don ganin an ceto matasa.

A cewar sa a shekara ta 1984 ne yasa kansa a cikin wata qungiya inda suke faxi tashin ganin sun taimakawa waxanda suke da buqatar hakan wanda burinsu shine na ganin an samu al’umma wacce take da tarbiyaa da xa’a wacce ba za’a sameta da rikici na tashe-tashen hankula ba wanda a lokacin da aka kamashi aka tsare shine wasu qungiyoyin sun tsaya amma yanzu da ya fito shine yake ci gaba.

 Manjo Hamza Al-Mustapha, ya kuma xan bada bayani halin quncin rayuwar da ya shiga a gidan Yarin na rashin samun abinci da ruwan sha wanda sai ya yi kwanaki sannan a ba shi sau xaya. Amma a cewar sa akwai wani Soja xan asalin jihar wanda yake taimaka masa da ruwa da abinci a boye amma Allah ya yi masa rasuwa a wani lokaci da yaje nemo masa qosai da ruwa.

A boye wannan sojan yake tsallakewa ya fita da Babur xinsa ya nemo min ruwan leda na Pure water da abinci wata rana da qosai ya kawo min inci ba tare da an ganshi ba” inji Al-Mustapha.

Cikin jimami da qarfin zuciya Al-Mustapha, yace ranar da wannan Soja zai rasu yazo ya gaishe shi yace Oga bari inje in nemo maka abinci bayan munyi sallama dashi ya fita yaje ya nemo min qosai da ruwa akan babur xinsa yana dawowa sai ya yi hatsari yaji ciwo kafin ayi masa allura tetanus ya shiga wanda shine ya yi sanadiyar ajalinsa

 Daga nan ne sai yace bayan hidimar wannan qungiya tasa taimakon iyalan wannan Soja suna daga cikin dalilansa na zuwa Gombe don ya taimakawa iyalan wannan Soja bisa yadda ya dinga masa hidima da har kan ya zamo sanadiyar rayuwar sa.

            

Xxx

No comments:

Post a Comment