Sunday, January 26, 2014

IDAN SANATAN MU DANJUMA GOJE YA KOMA APC ZAMU AIKA TAKARDA MU DAWO DASHI----INJI Yayari



Fagen Siyasa

IDAN SANATAN MU DANJUMA GOJE YA KOMA APC ZAMU AIKA TAKARDA MU DAWO DASHI----INJI Yayari

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Alhaji Ahmad Yayari, Shugaban ma’aikata ne na gidan gwamnatin jihar Gombe kuma dan asalin garin Chilo a karamar hukumar Akko, shi ya bayyana cewa da zarar Sanatan yankinsu Alhaji Muhammad Danjuma Goje, ya kuskura ya canja shega daga jam’iyyar PDP da aka zabe shi ya koma jam’iyyar adawa ta APC za su tura ya dawo domin basu yake wakilta ba.

Alhaji Ahmad Yayari, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a garin Kumo helkwatar karamar hukumar Akko a yayin da gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, yake rangadin ziyartar mazabun Sanatoci uku (Senatorial Tour)

A bayanan Ahmad Yayari, wanda tsohon Kwamishina ne har tsawon shekaru takwas a tsohowar gwamnatin da ta gabatan ya shaidawa gwamna Dankwambo cewa su al’ummar Gombe ta tsakiya musammam mutane garin Kumo basu amfana da romon democradiyya a gwamnatin baya ba domin duk girman garin Kumo babu aikin naira miliyan goma  a shekaru takwas din da gwamnatin tayi.

Ya kuma ce koda hanyar mararabar Zambuk zuwa Lubo da Hinna zuwa Gwani, a yankin Yamaltu Deba duk wash-wash ne akayi yanzu ya kirayi gwamna Dankwambo da cewa ya sake su domin dai dai suke da ba’ayi ba.

Shugaban ma’aikatan ya kara tabbatarwa gwamana Dankwambo cewa su mutanen Gombe ta tsakiya jam’iyyar PDP suke yi kuma tsohowar ta Bamanga Tukur, ba sabuwar ba amma Sanatan su da suka zaba Alhaji Danjuma Goje, ya tashi a gaban duniya yace shi dan sabuwar PDP ne wanda su idan dai a sabuwar PDP yake basu yake wakilta ba.

“ Yanzu haka muna jin rade-radin cewa zai koma jam’iyyar Hadaka wacce aka yi hadin gambiza ta APC  idan ya koma bamu yake wakilta ba don haka gwamna ka sani amma daga ranar da muka ji ya koma APC din mu al’ummar mazabar Gombe ta tsakiya kamar yadda muka kai shi haka zamu dawo dashi” inji Yayari.

Ya ci gaba da cewa yanzu lokaci bai zo tukuna amma yace suna jira suga ranar da zai koma APC din sannan kuma ya kara da cewa mutanen Gombe ta tsakiya sun gaya masa cewa kar ya yi Magana ya zuba ido kawai ya yi kallo suna jira suka wanda zai bada gidansa ko ofis a kafa ofishin sabuwar jam’iyyar ta APC.

Shi kuwa Kakakin Majalisar Dokoki ta jihar Gombe Alhaji Inuwa Garba, wanda yake wakiltar Yamaltu ta yamma cewa ya yi su mutanen yankin Yamaltu Deba wanda take Gombe ta tsakiya bakinsu daya da mutane Akko basa wata sabuwar jam’iyya in ba PDP ba.

Alhaji Inuwa Garba, ya kuma ce basu da zabi idan dai suna son ci gaba ne kuma basa son ace suna da wariya dole subi gwamna Dankwambo wajen sake bashi dama ya sake dawowa ya yi gwamna karo na biyu saboda gwamna Dankwambo, ya yi musu kokari an bai wa dansu Ministan Sufuri wanda kasafin kudin ma’aikatar sa yafi na yankin arewa maso gabas.

Sannna sai yace su mutane Gombe ta tsakiya musammam al’ummar Yamaltu Deba basa tare da wata sabuwar jamíyyar don su basa jin dari-dari ko ciwon kai balle su sha kafino ko paracitamol balle APC don haka su a yankin su PDP suka sani ba ruwansu da APC.

Da yake maida jawabi na godewa ga al’ummar jihar Gombe gwamna Dankwambo nuna fsrin cikinsa ya yi na irin hadin kai da goyon baya da suka bashi na karbar shugaban kasa a lokacin da ya ziyarci jihar a lokacin taron tattalin arzikin kasa na shiyar arewa maso gabas da ya gudana.

Daga nan sai ya yi kira na musamman ga matasa da su hada kai wajen neman abun yi don ganin sun dogara da kansu, anan ne ya yi kira da cewa su tashi su nemi keke Napep da tasi tasi da za’a bayar don samun hanyar samun abunyi su dogara da kansu.

                                                                   

                                                              xxx   

No comments:

Post a Comment