Abun Al’ajabi
Wata Mace Ta Haihu A Kasuwa A Garin Neman Inda
Mijinta Yake
Wata mata ‘yar asalin garin Lafiyan
Bare-bari dake jihar Nasarawa mai suna Maryam Sa’idu, ‘yar kimanin shekaru 30
da haihuwa wacce take aure a garin Baga, ta haihu a kusa da ‘yan gwan-gwan dake
babbar Kasuwar Gombe a lokacin da ta fito don nemo inda Mijinta yake wanda ya
bar gida watanni biyu da suka wuce bayan tarwatsa garin Baga a yankin Maiduguri
da ‘yan bindiga suka yi.
Aminiya,
menene sunaki kuma daga ina kika zo?
Maryam, sunana Maryam Sa’idu, ni ‘yar
lafiyan Bare-Bari ce amma ina aure a garin Baga dake Maiduguri.
Aminiya,
gaki a Gombe me ya kawo ki kuma wane
hali ki ke ciki?
Maryam- nazo garin Gombe ne don in nemi
mijina mai suna Abba, wanda ya bar gida Baga bayan tarwatsa garin da ‘yan
bindiga suka yi watanni biyu da suka wuce babu labarin sa.
Aminiya,
tun kamar yaushe kike Gombe kuma kin
gano inda mijin naki yake?
Maryam- nazo Gombe tun fiye da makonni
bakwai amma har yanzu ban samu labarinsa ba.
Aminiya,
lokacin da mijin naki zai bai gida ya
gaya miki inda zai je ne?
Maryam- bai gaya min ba wannan rikicin
da ya faru ne ya raba mu tun daga nan bamu sake haxuwa ba har yau, rashin sanin
halin da yake cikin ne yasa hankali na ya tashi yasa na fito yawon neman sa.
Aminiya,
me yasa ki ka zavi ki zo nemansa a Gombe
ko kin samu labarin yana Gombe ne?.
Maryam- ban ji labarin yana Gombe ba na
gaji da zama shiru ne shi yasa na zavi in zo Gombe kawai ko Allah zai sa in
dace saboda tafi kusa da inda na baro kuma bamu tafa rabuwa na tsawon lokaci
kamar haka ba tunda muka yi aure.
Aminiya,
kafin fi taho neman sa ko kinje gidan
iyayensa don shaida musu halin da kike ciki da kuma ce musu zaki fita neman sa?
Maryam- naje sai suka ce min suma basu
da labarin sa domin tun bayan barin sa suma basu da labarin inda yake basu san
ko rikicin ya rutsa dashi bane ko kuma yana nan da rai.
Aminiya,
a lokacin da ki kazo Gombe a ina kike kwana tunda baki san kowa ba?
Maryam- da nazo Gombe na samu gun wasu
masu sayar da maganin gargajiya ne ina kwana a wajensu, daga baya sai na nemi
inda zan je don in samu abun yi don in dinga samun abunda zanci ni da ‘ya ta
Larai shine wani ya tura ni wajen masu surfen shinkafa ina tsinta kuma ina taya
su aiki inaa samu xan abunda nake ci.
Aminiya,
yanzu gashi na ganki da Jariri a hannu
wanda bai wuce kawanaki ba shi kuma a ina kika samo shi?
Maryam- dama ina da ciki lokacin dana zo
Gombe, kuma ga ciki ga yunwa ga babu gun kwana mai kyau sannan bana samun
abinci ya ishe ni, ina gun tsintar shinkafar ne wani lokaci dana fita sai
naquda ta kamani har na haihu a tsakiyar wani layi ranar talatar da ta gabata, bayan
na haihu ne jama’a suka taimaka min suka kai ni cikin wani kango na zauna tare
da ‘yata da wannan Jinjiri da kake gani.
Aminiya, tunda baki da kowa a Gombe
kuma kina cikin wani hali idan satin haihuwar ya zagayo ya ya za kiyi da sunan
wannan Jinjiri?
Maryam- zan nemi mutanen da suke wajen
ne kawai su taimakeni a sa masa suna Ibrahim.
Aminiya,
tun daga lokacin da kika kasance a
wannan wajen kin samu kulawa daga wata qungiya ko hukuma?
Maryam- ban samu ba sai dai mai unguwar
wannan unguwa ta Herwagana ya sa an taimaka min da wasu yan kuxi naje asibiti
nan ma ‘yata Larai na kai aka duba ta saboda bata da lafiya tana fama da
sharattuwa, amma jaririn dana Haifa shi yana da qoshin lafiya sai dai kuma ni
kai na ina neman taimako domin ko sau xaya ban samu nayi wankan ba balle wankan
jego.
Aminiya,
yanzu idan kika samu taimakon da kike
nema daga jama’a koda baki iya gano inda mijin naki yake ba kina ga za ki iya
komawa garinku kuwa?
Maryam- eh zan koma amma nafi son su
taimaken da inda zan zauna yanzu tukun da kuma yadda zan ci gaba da kulawa da
kai na har Allah ya kawo qarshen wannan hali dana shiga.
Sai dai wani bawan Allah da yake sana’a kusa
da inda wannan mata take Alhaji Muhammad Kabir Hadija, ya shaidawa Aminiya
cewar wannan mata ta share fiye da watanni biyu a wannan waje yace za suyi iya
qoqarinsu don ganin sun haxa wannan mata da hukumar gidan Marayu ko ofishin
kula da jin xaxin al’umma na Social Welfare ko wata hukuma don ganin an taimaka
mata.
Xxx
No comments:
Post a Comment