Wata Budurwa ta sha fiya-fiya ta nemi kashe kanta saboda saurayi yaqi auren ta
Daga Rabilu Abubakar, a Gombe
Wata Budurwa mai suna Ummi Muhammad Muhammad, yar kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa dake zaune a bayan asibitin mata da qananan yara na Unguwar Idi kusa da gidan Alhaji Isma’ila Kashere, tayi qarar wani saurayinta mai suna Ali Salihu. Ummi Muhammad, ta yi qarar Ali Salihun ne a ranar 9 ga watan Janairun wannan shekarar a gaban kotun yanki ta Doma dake fadar jihar Gombe don a tilas ta shi ya aureta.
Tun farko kotun ta bata ranar 25 ga watan na janairu don ta dawo da niyar za’a tura a kirawo shi saurayin nata don jin ta bakinsa , inda ta kasa haquri taje ta samu wuqa zata kashe kanta nata aka qwace bata haqura ba ta sake nemo fiya-fiya ta sha don ta kashe kanta a ranar litinin 13 ga wata.
Wakilinmu ya samu zantawa da Ummi Muhammad, bayan da ta farfaxo daga kiximewar da tayi jim kaxan da xuramata madarar ruwa da saurayin ya yi don ya ceto rayuwarta inda ta bayyana masa cewa.
“ Shekaran mu xaya da fara soyayya da Ali Salihu, ina mutuwar son sa a raina har iyayena sun bashi ni amma yanzu sai yace min wai ba zai aure ni ba shine ni kuma nake ganin tunda ba zai aure ni ba gara in kashe kai na in hutu don ba zan iya rabuwa dashi ba” inji Ummi.
Ummi tace kafin yace ba zai aureta ba suna soyayya kuma tuni iyayensa suka nemi izinin aurenta a wajen iyayenta kuma aka bashi wanda kawai jira ake yi lokaci ya yi a xaura musu aure amma kwatsam rana xaya sai ya fito yace mata ya fasa auren.
“Rabuwa da duniya yafi zama alheri a guna akan in rasashi shi yasa daya furta min haka ni kuma na nemi wuqa zan kashe kai na da aka hana ni shine na nemo fiya-fiya na sha” inji ta.
Ta kuma ce tasan komai qaddara ne daga Allah amma a wannan lokacin ba wuhallinta bane shi saboda son da nake yiwa Ali ya wuce a kwatanta idan ba tsananin so ba mai zai sa in nemi kashe kai na.

No comments:
Post a Comment