Sunday, January 26, 2014

NDE TA HORAR DA MATASA FIYE DA DARI UKU SANA’OI HANNU DABAN-DABAN A JIHAR GOMBE



NDE TA HORAR DA MATASA FIYE DA DARI UKU SANA’OI HANNU DABAN-DABAN A JIHAR GOMBE

Daga Rabilu Abubakar, Gombe

Shugaban hukumar samar da ayyukan yi kai tsaye ta qasa NDE reshen Gombe Malam Mairiga Abdulqadir Madubi, shi ya bayyana hakan a lokacin da yake bayyanawa wakilinmu irin aikace-aikacen hukumar ta NDE a ofishinsa dake Gombe.

Malam Mairiga, yace amfani hukumarsu ta NDE shine ta koyawa Matasa da Mata harma da Yara sana’oin hannu wanda zai basu dama su dogara da kansu don su taimakawa jihar su da qasarsu dama ‘yan uwansu.

Yace a wannan shekara sun xauki Yara da dama suna koya musu sana’oi daban-daban inda suka xauki wasu guda hamsin kuma suna koya musu kiwon shanu da yadda zasu sarrafa abincin dabbobi da kuma yadda zasu kula dasu wanda yanzu haka suna nan a Tiken Dabbobi na tashar Dukku, kuma  an xinka musu yunifom.

Malam Mairiga Abdulqadir, yace za’a horar da Yaran ne na tsawon watanni huxu sannan a basu bashin kuxi su fara kiwon nasu suna saya suna kiwatata suna sayarwa suna cin riba, da haka har su fara biyan bashin da aka basu.

Ya kuma ce yanzu haka gwamnati ta samar da makarantu guda uku a kowanne mazavar xan majalisar dattawa da suke koyawa Yaran sana’oi na musammam  inda a Gombe ta tsakiya suka samar da xaya a garin Daxin-kowa yankin qaramar hukumar Yamaltu Deba, a kudancin Gombe kuma suka samar da xaya a garin Kaltungo sannan a arewaci kuma suka samar da ita a garin Bajoga, kuma Yara dari-xari suka xauka daga kowanne yanki.

Cikin sana’oin kuma yace akwai gyaran naura mai qwaqwalwa Kwamfuta da koya musu gyaran wayar Salula da girke-girke da Walda da sauransu, a cewar sa a kowacce sana’a sun xauki yara ashirin-ashirin cikin Yara xari an rarrabasu ashirin-ashirin kenan kuma yanzu sun fi wata biyu suna karvar horo kuma wata shida za suyi kafin ayayesu.

Sannan sai yace sun bi hanyoyin da ya kamata wajen zaqulo yaran basu bari anyi son kai wajen xaukarsu ba saboda idan basu sa ido ba za’a nuna son kai wajen xaukar wanda hakan bai kamata ba kuma yace suna sawa yaran ido don ganin sun tsaya sun koyi sana’oin domin duk wanda yake wasa bai tsaya ya koyi sana’ar yadda ta dace ba zai yi wuya su yaye shi.

Daga nan sai ya bayyana cewa idan Yaran suka tsaya suka koyi wannan sana’oin  za suci moriyar ta domin tafi aikin gwamnati kamar yadda yace qasashen turawan da suka ci gaba talaka shi yake aikin gwamnati kowa yafi dogara da sana’oin hannu ne wanda sune suke vunqasa musu tattalin arzikin qasashen su.


xxx

No comments:

Post a Comment