RAHOTON
MUSAMMAM
Garin Tula a karamar hukumar
Kaltungo ya samu asali da can baya ake kiran shi Wure- Titilo da suke da
wani Kogon dutse inda ‘yan kabilar ta Tula suka yi amfani dashi wajen boye
kananan Yara da Mata da Nakasassu a lokacin yakin su da abokan gaba a
shekarar 1906 inda su kuwa Matasa da Jarumai kan fito fagen daga don tarar
abokan gaba.
Shi dai wannan dutse na Tula yana
nan ne a garin Tula dake Yankin karamar hukumar Kaltungo dake jihar Gombe
kimanin kilimita 120 daga fadar jihar, wanda yan kabilar ta Tula suka kasu gida
uku Tula Yiri da Tula Baule da kuma Tula Wange.
Wakilinmu ya yi tattaki zuwa
garin na Tula ya kuma samu ganawa da Dagacin Tula Wange Mista Andrew Aliyu mai
shekaru 65 inda ya bayyana masa cewa Kakannin su suna hawa kan wannan dutse
nasu don samun kariya daga abokan gaba a lokacin yaki
Mista Andrew ya kara da cewar wannan
kogon dutse da suke sanya kananan Yara da Mata a lokacin yaki kofar shigar shi
karama ce amma cikin shi yana da fadi saboda kankantar kofar babu yadda abokan
gaban su a wancan lokacin zasu gane cewar mafaka ce gare su mutanen Tula.
Yaci gaba da cewar wannan kogon
dutse yana daukar daruruwan jama’a kuma akwai Rijiyar da suke amfani da ita
wajen shan ruwa a cikin kogon dutsen a lokacin da suke gudun hijira a ciki.
Har ila yau wakilinmu yace kogon
dutsen yana da nisan Mita dari 200 ne daga mashigar garin na Tula da take kan
wani tsauni, Wure Titilo dai ya kamata ace ta zama tana daga cikin
wuraren tarihi na kasa amma hakan bai yiwu ba saboda noma kawai ake yi a wajen
kuma da Damina ba za ka iya gane bakin kogon dutsen ba sai a lokacin rani
saboda ciyawa ta rufe wajen.
A bisa tarihin kasar Tula duk
yake-yaken da suka gubza da abokan gaba babu wanda ya gudana a cikin Masarautar
garin duk a waje da masarautar ya auku.
Dagacin na Tula Wange Andrew Aliyu,
ya kara da cewar al’ummar Tula din sunyi yaki ma da Mutane garin Misau dake
jihar Bauchi inda suka bullo da wata dabara a lokacin yakin ta hanyar gurbatawa
mutane Misau din mashayar Ruwan su da guba wanda yin hakan ya basu nasarar cin
su da yaki har suka cire kan sarkin Misau din suka dawo dashi garin Tula suka
ajiye don tarihi.
xxxxx

No comments:
Post a Comment