Sunday, January 26, 2014

Yaushe Danjuma Goje Ya Zaman Uban PDP a Gombe Bayan Gwamna shine Uban Jam’iyya a jihar sa ---- Castic

Daga Rabilu Abubakar, a Gombe Alhaji Abdullahi Ibrahim Jalo wanda ake kira Castic shine mataimakin kakakin jam’iyyar PDP ta qasa, ya yi taron manema labarai a Gombe inda ya musanta cewa ba Danjuma Goje bane Uban PDP a jihar Gombe. Aminiya, me wannan taro da ka kira na ‘yan jaridu ya qunsa. Sunana Abdllahi Jalo, na kira wannan taro ne domin in mayar da martani wa tsohon gwamnan Gombe Danjuma Goje, a matsayina na mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na qasa bisa kalaman da ya furta a lokacin da yazo shari’ar sa da kuma irin abubuwan da suka faru, domin da zuwansa ya tara matasa xauke da takubba da adduna suna yiwa mutane barazana a gari bayan shi ba gwamna ba ne inda yake so ya sake lalata matasan bayan an farfaxo da tarbiyarsu. Kamar kuma yadda yace a lokacinsa ne ya qwace mulki daga hannun ANPP ai ba qwace mulki ya yi ba Allah ne ya karvi mulki daga hannun Hashidu a ANPP ya bashi kuma ai ba shi kaxai ya yi wannan gwagwarmayar ba ni ma ina cikin wannan tafiyar domin nasa iya siyasa ta da kuxi na. Aminya, yanzu za’a iya cewa PDPn Gombe sun fito fili kenan suna faxa da Goje? Abdllahi Jalo, ba faxa ake yi dashi ba ai gwamna mai ci a jiha Ibrahim Hassan Xankwambo, yaushe ma ya fito ya yi magana balle ace yana faxa da Goje, ai shi Goje ne ya fito yake neman faxa domin yana cewa shine Uban duk ‘yan PDPn Gombe wanda shi ya qwace mulki daga ANPP ya kawo PDP abunda nake so ka sani shine mu ba qwace muke yi ba zave akayi muka ci zave amma dai na yarda da shi ya jagorance mu a lokacin. Aminiya, menene laifin abunda Goje, ya yi a tsarin jam’iyyar ku ta PDP? Abdllahi Jalo, lafinsa shine ya fito yace akwai sabuwar PDP harma ta qwace Gombe shifa Sanata ne mai ci kuma mutum ne mai ilimi ya kamata yasan akwai doka, wacce ita ta kai shi ya wakilci mutane kuma a PDPn yaci zave wacce Bamanga Tukur, yake shugabanta ba sabuwar PDP ba ashe kuwa in haka ne daga furta wannan magana tasa ya kamata a kamashi saboda ya sava doka. Aminiya, yanzu wane hukunci kuke shirin tanada akan sa? Abdullahi Jalo, hukuncin da zamu xauka akansa shine za muje wajen Uwar Jam’iyya mu rubuta mata takarda muce mata ga abunda ya yi sannan a duba a kira shi ya amsa tambayoyi domin tuni an naxa kwamtin laxabtarwa a qarqashin jagorancin Umaru Dikko, amma yana da kyau mutane su sani kunxin tsarin mulkin PDP ya tabbatar da cewa ba’ayin gwamna biyu a jiha, don haka shugaban jam’iyya ko Ubanta a jihar Gombe shine gwamna Ibrahim Hassan Xankwambo, Goje ya zone wataqila da wata manufa ta komawa zuwa jam’iyyar APC shi yasa, hakan kuma takalar faxa ne don baka tava jin gwamnonin da suka yi shekara takwas suka sauqa suka kawo waxanda suka gajesu suna irn wannan faxan da iyayen gidansu ba ko kaji ance ma gwamnan Borno ya yi faxa da wanda ya kawoshi ko gwamnan Kwara, bari kaji wani abu anyi ‘yan takarar gwamna fiye da goma a Gombe wanda Goje ya yaudare su irn su Faruk Bamusa da Audu Hamma Saleh da sauransu har wata rana a wajen xaurin auren Babban Sufetan ‘yan sanda na qasa a Abuja Danjuma Goje, yaje ya gaisa da IBB sai ya miqawa Faruk Bamusa hannu sai Faruk yaqi bashi hannu magana ta tashi aka tambaya sai yace ya damfareshi ne ya karvi kuxinsa ya hanashi kujerar gwamna. Aminiya, kana nufin wannan kujera ta gwamna sayarwa Xankwambo kenan aka yi tunda an karvi kuxin wasu an hansu sai Xankwambo? Abdullahi Jalo, Ni xai ban faxi haka ba nasan dai na Faruk Bamusa, da yake qanina ne kuma nima an nuna min wata bishiya ance in ajiye miliyan hamsin wai za’a bani kujerar Sanata nace masa a’a an karvi kuxin Audu Hamma Saleh shi yasa kullum yake Allah ya isa ga Dahiru Buba Biri, kwamishina wanda bai da kuxi amma shima sanda aka karvi kuxin sa. Aminiya, daga qarshe kowa yasan cewa yanzu babu Kalare a Gombe amma kuma kace Goje ya taho da Kalare daga ina ya taho dasu? Abdullahi Jalo, hayarsu ya yi tunda dama yasan mutanensa ‘yan ina da kisa, dama ai makashi yasan inda makashi yake. Mun gode.

No comments:

Post a Comment