Friday, January 24, 2014

NINE UBAN DUK WANI XAN PDP A JIHAR GOMBE-------------SANATA DANJUMA GOJE

NINE UBAN DUK WANI XAN PDP A JIHAR GOMBE-------------SANATA DANJUMA GOJE Daga Rabilu Abubakar, a Gombe Dandazon magoya bayan tsohon gwamnan jihar Gombe ne kuma Sanata mai wakilta mazavar Gombe ta tsakiya a majalisar Dattawa ta qasa Sanata Muhammad Danjuma Goje, ne suka tare shi a lokacin da ya dawo gida daga Abuja don ci gaba da sauraron shari’ar da ake masa bayan sun gudanar da mitin xinsu na sabuwar jam’iyyar PDP a Abuja sannan kuma yace shine Uban duk wani xan PDP a jihar Gombe. Sanata Goje, ya bayyana hakan kuwa a ranar Litinin xin da ta gabata a fililin sauqa da tashin jiragen sama na qasa da qasa dake garin Lawanti a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai. Mai girma Sanata kasancewar daya daga cikin jiga-jigan sabuwar jam’iyyar PDP me zaka ce dangane da mitin xin da kuka gudanar jiya a Abuja Eh mun gudanar da taro na sabuwar PDP a Abuja amma da yake muna da tsari akwai tsarin uwar qungiya wacce ta qunshi gwamnoni guda bakwai da wasu Sanatoci kaxan da kuma wasu tsofaffin gwamnoni kaxan amma mitin xin da muka yi jiya kashi biyu ne da farko anyi na uwar qungiya da kuma yan majalisun tarayya da Sanatoci waxanda suke goyon bayan wannan qungiya a gidan gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso a Asokoro, da aka gama sai aka shiga mitin na asalin uwar qungiya saboda a dubi yanayin siyasar Najeriya muga me za muyi domin mu taimakawa Najeriya a samu ci gaba da dorewar zaman lafiya. Ko a mitin xin naku kun tattauna yiwuwar ficewarku daga PDP ko koma wata sabuwar jam’ iyya Danjuma Goje, bani da damar bayar da amsa akan wannar Magana domin bani bane mai Magana da yawun qungiyar ba. Ana maganar cewa akwai sabuwar PDP ko babu ita a jihar Gombe kuma kace kai ne Uban PDP ya ake ciki Danjuma Goje,kai ma kace nine Uban PDP ko eh mana nine Uban PDP a jihar Gombe tunda ai da ANPP ce take mulki a jihar Gombe a shekara ta 2003 ne a qarqashin shugabancina na jagoranci yaqi da ANPP sanda muka qwace mulki daga hannunsu Gombe ta dawo jihar PDP, duk wani mai burgar siyasa a jihar Gombe yana cewa shi xan PDP ne to qarqashina yake domin ni shugabanci wannar rigima har aka kafa gwamnatin PDP a jihar Gombe har wasu suke tinqaho suna cewa sune ‘ yan PDP yau babu wani wanda yafi zama xan PDP yau a jihar Gombe kowanene shi. Mai girma Sanata mai zaka cewa magoya bayanka da suka taro ka a filin jirgin sama yau a jihar Gombe. Ina cike da farin ciki matuqa wanda har ya kai ga ba zan iya bayyanawa saboda yadda naga xan adam a wannan wuri da suka zo taroni manya da yara tsofaffi da matasa a gaskiya ni ban xauka abun ya kai haka ba domin ni nazo shari’a ne ba nazo siyasa ba amma ina qara godiya ga Allahu S.W.T da yasa mutanen Gombe suka san nayi musu ayyuka na gari a lokacin da nake gwamna har yasa yanzu suka shirya tara ta na musammam a filin jirgin sama ai kaga bana gwamna kuma na jima banzo Gombe amma nayi mamakin yadda naga xan adam a wannan waje wanda duk wasu sharrance-sharrance da ake yi mun bai sa jama’a sunyi qasa a guiwa wajen zuwa su tareni ba nagode musu qwarai. Mun gode Sanata Danjuma Goje, nagode muku.

No comments:

Post a Comment