11/04/2011
RAHOTON KAI LITTATTAFAN BASHIR OTHMAN TOFA
JIHOHI BAKWAI NA AREWACIN NIJERIYA
Kamar yadda aka ba wa kamfanin Gidan Dabino International alhakin tallata littattafan Bashir Othman Tofa guda takwas a jihohin arewacin Nijeriya da }asar Nijar da kuma kai littattafan zuwa ma’aikatun ilmi na jihohin domin a tallata musu don su saya. Mun fara da jihohin bakwai da kuma Yamai }asar Nijar: Ga sunanyen garuruwan:
1. Kano
2. Katsina
3. Zamfara
4. Sokoto
5. Kebbi
6. Neja
7. Abuja
8. Kaduna
9. Zariya
10. Yamai Nijar
Ranar Alhamis 16/12/2010, muka fara tafiya, inda muka nufi jihar Katsina, kafin mu shiga Katsina mun tarar da ‘yan siyasa suna fa]a, ‘yan sanda kuma sun tare hanya suna ta watsa tiyagas, sun hana shiga garin Katsina, mu ma mun sha tiyagas iya rabonmu, (ni da direba Abdullahi) kuma mun tsaya carko-carko a cikin gayyar ‘yan siyasar, kafin daga baya ‘yan sanda su bu]e hanya mu shiga cikin Katsina.
Mun fara da ma’aikatar ilmi inda muka je ofishin kwamishina don isar da sa}on, amma a lokacin da muka je kwamishina bai zo ofis ba sai muka mi}a littattafan saiti guda da wasi}ar neman sayen littattafan ga sakataren kwamishinan, ya sa mana hannu a kwafin tamu wasi}ar don nuna shaidar cewa ya amshi littattafan da wasi}ar.
KVC Bookshop
Daga nan muka nufi kantin sayar da littattafai na KVC Bookshop a kan titin Yahaya Madaki, inda muka bayar da littattafan saiti 50.
Ziyara Bookshop
Sai kuma muka isa Ziyara Bookshop da ke kan titin IBB, muka ba su saiti 10. Bayan mun yi sallar magariba sannan muka nufi jihar Zamfara, inda muka kwana.
Ranar Juma’a 17/12/2010 muka je ofishin kwamishinan ilmi na jihar Zamfara inda muka bayar da littafi saiti ]aya tare da takardar neman sayen littattafan, shi ma a nan kwamishina bai shigo ofishin ba sai sakatarensa muka baiwa, ya sa mana hannu a kan kwafin wasi}armu don nuna shaidar ya amshi wannan sa}on littafi da wasi}ar.
Mai Litttafi Bookshop
Daga nan muka nufi kantin sayar da litattafai na Mai Litttafi Bookshop da ke kan titin Ahmad Bello kusa da gidan Alhaji Bala Waiman. Saiti uku kawai suka kar~a na littafin. Sai muka nufi Sokoto don ko ma sami ma’aikata a ofis kasancewa ranar Juma’a ce.
Mun iso Sokoto daf da lokacin tafiya masallacin Juma’a, don haka muka iske ba kowa a ofishin kwamishinan ilmi, muka zauna muka jira ko za su dawo daga wajen salla amma ina, ba wanda ya dawo, don haka muka nufi masauki, (ranar dai ba mu sami sallar Juma’a ba).
Abdullahi mai Littattafai
Ranar Asabar 18/12/2010 da safe muka nufi babbar kasuwar Sokoto wajen Abdullahi mai Littattafai, wanda muka bai wa saiti 50 na littattafan.
Sifawa Bookshop
Daga nan sai Sifawa Bookshop da ke kan titin Atiku, inda ya kar~i saiti 5 na littattafan. A Sokoto mun bar sa}on littattafan ne ga wani mutuminmu wanda ya kai mana sa}on ga kwamishina kuma ya kawo mana takardar shaidar sa}on ya isa ofishin kwamishinan, wanda PA ]in kwamishina ya amsa ya sa hannu a kan takardar ranar Litinin 20/12/2010.
Ranar Lahadi 19/12/2010 ne da rana muka nufi jihar Kebbi inda muka kwana a can. Da safiyar Litinin 20/12/2010 muka je ofishin kwamishina inda muka bayar littattafai saiti biyu saboda an nemi a yi hakan ne don a bai wa kwamishina saiti ]aya saboda wata tattaunawa da muka yi da PA na kwamishinan. Saboda wannan tattaunawar da muka yi ya sa muka da]a kwana a garin inda muka ga duk masu ruwa da tsaki wajen sayen littattafai a jihar inda muka zauna muka yi tsayayyiyar magana a kan yadda za a gudanar da wannan sayen littafi da kuma abin da za a ba su in har an saya.
Mun shiga kasuwa don bayar da tallan littafin ga wasu masu kantunan sayar da littattafai, amma abin bai yiwu ba saboda matsalar farashin ya yi musu yawa, don haka a jihar Kebbi ba mu bayar da tallan littafi ko ]aya ba.
Ranar Laraba 22/12/2010 ne da safe muka bar jihar Kebbi inda muka nufi jihar Neja, inda muka fara da ma’aikatar ilmi, muka isar da sa}on littattafan da wasi}ar, inda PA ta kwamishina ta amsa, sannan muka yi mata ]an ihsani don ta ba mu hasken lamarin kasancewar ba mu san kowa ba a wajen. Ta gaya mana yadda za mu yi don haka muka tafi wajen babban sakatare na ma’aikatar ilmi na jihar muka gaya masa abin da ke tafe da mu da kuma fatanmu, muka yi bu]a]]en zance da shi, sannan ya sanar da mu yanzu ba abin da zai yiwu sai dai bayan za~e.
KC Bookshop
Daga nan muka shiga kasuwar Gwari, inda muka je KC Bookshop, shi ne babban kantin sayar da littafin Hausa a wannan gari. Ya kar~i saiti biyu don ya jarraba ya gani don ya koka kan farashin ya yi tsada.
Ranar Alhamis 23/12/2010 da safe muka nufi Abuja, inda muka fara da ofishin babban sakatare na ma’aikatar ilmi ta birnin Abuja, ba mu same shi ba sai dai muka bayar da sa}on ga PA ]insa, ta kuma sa mana hannu a kwafin wasi}armu shaidar ta amshi sa}on.
Ibrahim Lawal mai Aminiya
Daga nan muka nufi kusa da ofishin ABC Transport, da ke Utaka, a birnin Abuja inda muka bayar da saiti biyar ga Ibrahim Lawal mai Aminiya.
Garki Super market
Mun je kantin Garki Super market da ke Area 11, kan titin Ahmadu Bello, sun kar~i saiti 3.
Sahad Store Abuja
A Sahad Store da ke Uke Street a Garki Area 11, ba mu sami mai kula da harkar littattafai ba, sai dai mun yi waya da shi ya ce mu bar masa saiti 1 ya gwada ya gani. A ranar muka bar Abuja muka nufi Kaduna, don washegari Juma’a ce kada mu rasa samun ma’aikatar ilmi ta Kaduna.
Destiny Bookshop
Ranar Juma’a 24/12/2010 da safe muka je ma’aikatar ilmi, ba mu sami kwamishina a ofis ba, sai PA muka bai wa, ya sa mana hannu, ya kar~a. Muka kuma nemi shawarar sa ta inda za mu taro maganar, ya gaya mana, daga nan muka nufi ofishin daraktan ilmi na ma’aikatar, muka tattauna da shi, daga nan muka bar ma’aikatar muka nufi titin Ahmadu Bello, a ginin Leventis, inda muka kai wa Destiny Bookshop littattafai, ya amshi saiti 10.
Kola Bookshop
Ranar Lahadi 26 ne muka dawo gida Kano, kasancewar ranar Lahadi kantin Kola Bookshop ba sa fitowa, don haka ba mu sami ba su littafin ba a wanan karo.
Bayan mun dawo gida ne da wasu kwanaki sai aka kira ni daga Educational Resource Centre (ERC) Kaduna cewa littattafan da na kawo ma’aikatar ilmi sun iso gare su kuma suna sashen da zai duba su ya ga cancantar su da kuma inda ya kamata a karanta ko a saye su, don haka ana so in zo da }arin saiti 3, don haka }a’idarsu take, kuma za a biya ku]in duba kowane littafi 3,000, na kuma sanar da Alhaji Bashir Tofa ya yi min izini, na sake komawa Kaduna na cika wannan umarni. A wannan lokacin komawa Kaduna ne na tafi da littattafai na biya ta garin Zariya na kai wa Kola Bookshop da ke Park Road, ya kar~i saiti 5.
Edition Gashingo
Mun aika wa da kamfanin Gashingo da ke birnin Yamai ta }asar Nijar littattafai saiti 50
Al’amin Bookshop
A jihar Kano a waje daya kawai muka bayar da littafin, wato a kasuwar Sabon Gari, mun bai wa Al’amin Bookshop saiti 10, yawancin manyan kantunan da za mu baiwa an ce an kai musu, kamar Sahad da Jifatu da zamani da Country Mall, don haka ba mu kai musu ba.
Adadin littattafan da muka rarraba a kantuna da kasuwanni:
Kano: Al’amin Bookshop Saiti 10 littafi 80
Katsina: KVC Bookshop saiti 50 littafi 400
Ziyara Bookshop saiti 10 littafi 80
Zamfara: Mai littafi Bookshop saiti 3 littafi 24
Sokoto: Abdullahi mai Littafi saiti 50 littafi 400
Sifawa Bookshop saiti 5 littafi 40
Kebbi: Babu wanda ya kar~a
Neja: KC Bookshop saiti 2 littafi 16
Abuja: Garki Super market saiti 3 littafi 24
Sahad Store saiti 1 littafi 8
Ibrahim Lawan Mai Aminiya saiti 5 littafi 40
Kaduna: Destiny Bookshop saiti 10 littafi 80
Yamai Nijar: Edition Gashingo saiti 50 littafi 400
Zariya: Kola Bookshop saiti 5 littafi 40
Jimlar littattafan da muka rabar su ne: 1,632
Ku]insu ya kama Naira Miliyan [aya da Dubu [ari Shida
da Talatin da Biyu N1.632,000
Gaba ]ayan ltitattafan da muka kar~a a wannan zagaye na farko (set 250) wato guda 2,000 ne don haka yanzu akwai sauran littattafai 368 a wajena.
Bayanai daga masu sayar da littattafai daga jihohi
Na kira mutanen da muka kai wa littattafai a dukkanin jihohin nan da kuma }asar Nijar.
{asar Nijar, abin da suka sanar da ni, lokacin da na tuntu~i manajar kasuwanci Edition Gashingo, wato Nasifa Ibrahim ta hanyar waya da kuma e-mail, ta gaya min ko littafi guda ]aya ba su sayar ba.
Abuja, Ibrahim mai Aminiya ya ce Alhamdu lillahi littafi ya samu kar~uwa ya kusa sayar da wanda ya amsa saiti 5, an sayar da Kimiyya da Al’ajuban Al}ur’ani guda hu]u N4,000, Amarzadan da Zoben Farsiyas guda ]aya N800, Amarzadan a Birnin Aljanu guda 4 N3200, Rayuwa Bayan Mutuwa guda hu]u N3200, Gajerun Labarai guda uku N3000, Mu Sha Dariya guda 4 N4000,Tunaninka Kamanninka guda uku N3,900, Kimiyyar Sararin Samaniya guda uku N4500. Jimla an sayar da litattafai guda 26, kudin su N26,600
Garki super market na yi magana da mai kula da lamarin wadda dama ita ta amshi littattafan, wato Halimat, ta ce an sayar da na N800 guda 10, an sayar da na N1,000 guda 4, na N1,300 guda ]aya, na N1,500 guda ]aya. Don haka an sayar da litattafai guda16, wanda ku]in su ya kama N14,800.
Sahad store ban sami Sulaiman mai kula da littattafan ba don haka ban ji komai game da saiti ]ayan da aka ba su ba.
Sokoto: Abdullahi mai littafi ya ce ana son littafin amma batun ku]i ne mutanen suke kasa saye, don haka ‘yan kwayoyin kawai ya sayar kamar haka: Tunaninka Kamanninka guda 2, N2600, Gajerun Labarai guda daya N1000, Mu Sha Dariya guda ]aya N1000, Amarzadan A Birnin Farsiyas guda ]aya, N800, Amarzadan Da Zoben Aljanu guda ]aya N800. Jimla an sayar da litta guda shida ku]insu N6,200.
Sifawa Bookshop ban sami magana da su ba saboda layin a rufe yake kusan duk lokacin da na kira.
Katsina: KVC Bookshop su ne suka sayar da mafi yawa, don sun sayar da set 10, wato littafi 80, wanda ku]insa ya kama N80,000.
Ziyara Bookshop ya bayyana cewa ya sayar da Kimiyya da Al’ajuban Al}ur’ani guda biyar N4,000, Mu Sha Dariya guda biyu N2000, Tunaninka Kamanninka guda ]aya N1,300. Jimla an sayar da litattafai guda 8, ku]insu N7,300
Zamfara: Mai littafi Bookshop, ban sami layinsa ba a rufe har lokacin da na gama ha]a wannan rahoto.
Kano: Al’amin Bookshop ya bayyana min cewa an fi sayen tunaninka kamanninka, don a halin yanzu ya sayar da guda shida N7800, Rayuwa Bayan Mutuwa guda ]aya N800, Amarzadan A Birnin Aljanu guda ]aya N800, Amarzadan Da Zoben Farsiyas guda ]aya N800, Kimiyyar Sararin Samaniya guda ]aya N1,500 Kimiyyar Da Al’ajuban Al}ur’ani guda ]aya N800, an sayar da littafi guda goma sha ]aya, ku]insu N12, 500.
Neja: Ban sami magana da su ba don haka ban san halin da ake ciki ba a can sai dai nan gaba in na same su.
Kaduna: Destiny Bookshop, sun gaya min an sayar da Kimiyya da Sararin Samaniya guda ]aya N1,500, Tunaninka Kamanninka guda uku 3,900. Jimla an sayar da litattafai guda hu]u ku]insu N5,400
Duk wa]annan wurare tuntu~ar su na yi a waya, sai Nijar da muka yi waya muka yi e-mail.
Jimlar ku]in kayan da aka sayar sun kama N152,000
SAURAN JIHOHIN DA ZA MU JE BAYAN AN GAMA ZAB|E
1. Jigawa
2. Bauchi
3. Gombe
4. Yola
5. Maiduguri
6. Yobe
Wa]annan jihohi su ne sauran jihohin da za mu je don kai wa]annan littattafai ga ma’aikatun ilmi da kantunan sayarwa. Abin da ya sa ba mu yi wannan tafiya ta sauran jihohin gabacin arewacin Nijeriya ba shi ne, mun sa rana za mu tafi sai muka ji ana fa]a a jihar Gombe ana rikincin ‘Yankalare, sai muka ]aga muka ce sai wutar ta lafa. Bayan wannan ta lafa sai kuma rikici a Bauchi. Maiduguri kuwa dama ta zama fagen fama.
Daga }arshe dai muka bar tafiyar sai bayan za~e, tun da an ce turbar lafiya a bi ta da shekara, don muna zaton bayan za~en abubuwa za su yi sau}i.
Mun sanya tallan guraren da za a sami wa]annan littattafai a cikin sabon fim ]in kamfanin Gidan Dabino da ya fito kasuwa ranar Laraba 07/07/2011 mai suna SANDAR KIWO.
KARIN BAYANI
A tare da wa]annan takardu na ha]o da hoton takardun bayanin bayar da littattafan ga ma’aikatun ilmi da kuma kantuna da ‘yan kasuwa, da kuma rasitai shaidar karbar littattafan
Ado Ahmad Gidan Dabino,
Shugaba Daraktan Gudanarwa